
Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin sakin tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo Dasuki da Omyele Sowore mai jaridar Saharareporters.
Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayar da sanarwar a ranar Talata.
Malami ya ce gwamnati ta amince da sakin mutanen biyu ne domin mutunta hukuncin kotuna daban-daban na neman belin da suka yi.
Sanarwar ta ce ” ofishina ya zabi ya martaba umarnin kotu, inda kuma a waje daya muna duba yiwuwar daukaka kara ko kuma waiwayar neman beli da kotuna da dama suka yi.”
An bukaci mutanen guda biyu da su kame daga aikata abubuwan da za su janyo tayar da zaune tsaye da kuma cikas ga tsaron kasa sannan kuma ka da ya yi tarnaki ga shari’ar da ake yi musu bisa dokokin kasa.”