Gwamnatin jihar Kogi ta yi kira ga mazauna jihar da kada su shiga zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da aka shirya gudanarwa.
Akwai dai rahotanni dake cewa wasu matasa sun shirya gudanar da zanga-zanga a tsakanin ranakun 1-15 ga watan Agusta domin nuna damuwarsu kan halin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Kingsley Fanwo kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce gwamnatin jihar na tare da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a ƙoƙarin da take na gyara tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce tuni ƙoƙarin da gwamnatin take ya fara haifar da sakamako mai kyau duba da yadda gwamnatin ta mayar da hankali wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya, noma, ilimi da kuma masana’antu .
Ya ƙara da cewa gwamnan jihar, Usman Ododo na cigaba da ganin sakamakon ƙoƙarin na gwamnatin tarayya ya isa lungu da saƙoa na jihar.
” A matsayin mu na ƴan ƙasa nagari akwai buƙatar mu goyi bayan gwamnati a dukkan mataki domin ta yi maganin matsalolin da suka hana mu walwala,” ya ce.
Ya cigaba da cewa zanga-zanga a wannan lokacin tamkar yin ƙafar ungulu ne kan shirin na gwamnati kuma yunkuri ne jefa ƙasarnan a cikin irin mummunan yana yin da ta shiga a lokacin zanga-zangar ENDSARS.