Gwamnatin Kaduna za ta gina gidaje 10,000 a cikin shekaru 4

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta gina gidaje masu sauki 10000 a cikin shekaru huɗu masu zuwa.

Rabiu Inusa babban sakatare a ma’aikatar gidaje da bunƙasa birane ta jihar Kaduna, shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a wurin taron hukumar filaye, gidaje da bunkasa birane ta ƙasa wanda aka gudanar a jihar.

Yunusa ya ce akwai karancin gidaje a Najeriya sosai kuma gwamnatin jihar Kaduna ta shirya shawo kan lamarin.

Ya ce gwamnan jihar Uba Sani ya na kokarin aiwatar da wani shiri na gina gidaje a faɗin ƙananan hukumomin jihar 23.

Ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta gayyaci wata kungiyar agaji da ƙasar Qatar inda za su samar da gidaje 500 ga mutane masu karamin karfi.

Related Articles