Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar ɗaliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar ƙyanda.

A wata sanarwa ranar Litinin, A’isha Umar babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce an tsawaita hutun ɗaliban ne domin gwamnati ta samu damar yiwa dukkanin yaran jihar allurar riga-kafi.

Ta bayyana rashin jin ɗaɗin ta kan damuwar da hakan zai kawo inda ta bayyana cewa  wasu daga cikin yaran sun riga sun kamu da cutar.

Tun da farko an shirya cewa makarantu jihar ta Adamawa za su fara zangon karatu na uku ranar 06 ga watan Mayu amma yanzu aka ɗaga zuwa ranar 13 ga watan Mayu.

A cikin watan Afrilu aka bada rahoton mutuwar yara 19 a ƙaramar hukumar Mubi ta jihar sakamakon cutar ta ƙyanda.

More from this stream

Recomended