Bayan dan jinkirin da ya yi na gabatar da jawabi a cikin dare ta tashar talabijin, Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana sunayen sabbin ministocin gwamnatinsa, inda rabinsu mata ne.
A wannan karon ya rage yawan ministocin daga 36 zuwa 28, yana mai cewa ministocin sun yi yawa sosai, a don haka ne ya yanke shawarar ragewar.
Kazalika Cyril Ramaphosan wanda aka zabe shi a matsayin shugaban Afirka ta Kudun a babban zaben kasar na ranar 8 ga watan Mayu, ya kuma hade wasu ma’aikatun kasar 14 zuwa bakwai.
Misali ya hade ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu da ta Bunkasa Tattalin Arziki wuri daya.
Haka kuma ya shigo da sabbin jini matasa a cikin majalisar amma kuma ya rike wasu daga cikin manya kuma kwararru daga cikin tsoffin ministocin nasa.
Daga cikin fitattun, Tito Mboweni, zai ci gaba da zama a ma’aikatar kudi, da kuma Pravin Gordhan a ma’aikatar kula da kamfanonin gwamnati.
A jawabin nasa Shugaba Ramaphosa ya ce a karon farko a tarihin Afirka ta Kudun rabin yawan ministocin kasar za su kasance mata.
Babbar jam’iyyar hamayya ta kasar Democratic Alliance, ko DA, a takaice ta yi maraba da sabbin nade-naden ministocin.
Amma kuma ta yi gargadin cewa da kamata ya yi kuma Mista Ramaphosan ya rage yawan mataimaka ko kananan ministoci su ma.
Shugaban mai taka-tsantsan da nazari wajen tafiyar da harkokinsa ya bayar da mamaki ga mutane da dama sakamakon nada jagorar daya daga cikin sabbin jam’iyyun hamayya na kasar a cikin majalisar ministocin.
Patricia De Lille ta jam’iyyar hamayya, ta Good, ta samu matsayin ministar bunkasa kayayyakin jin dadin jama’a, wanda nadin ya shammaci da dama.