
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sanya hannu kan wata doka ta musamman da ta sauya fasalin ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16.
A cewar Sulaiman Bala Idris mai magana da yawun gwamnan wanda ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an dauki matakin ne domin rage barna a gwamnati da kuma kawar da yin aiki iri daya da wasu ma’aikatun ke yi.
Ya ce gwamnan ya rattaba hannu kan dokar ne a dakin taron majalisar zartarwar jihar ranar Alhamis a Gusau.
Sabababbin ma’aikatun da aka amince da su sun haɗa da ma’aikatar:
- Noma
- Kasafin kudi da tsare-tsare
- Kimiyya da Fasaha
- Muhalli da Arzikin ƙasa
- Kudi
- Lafiya
- Kasuwanci
- Cikiniki da Masana’antu
- Gidaje da Bunkasa Birane
- Shari’a
- Al’adu da Yada Labarai
- Kananan Hukumomi da Masarautu
- Addinai
- Mata da Cigaban Jama’a
- Matasa da Wasanni
- Aiyuka da Ababen more rayuwa
- Tsaro da Harkokin Cikin Gida