Gwamnan Zamfara ya rage yawan ma’aikatun jihar zuwa 16 daga 28

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sanya hannu kan wata doka ta musamman da ta sauya fasalin ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16.

A cewar Sulaiman Bala Idris mai magana da yawun gwamnan wanda ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an dauki matakin ne domin rage barna a gwamnati da kuma kawar da yin aiki iri daya da wasu ma’aikatun ke yi.

Ya ce gwamnan ya rattaba hannu kan dokar ne a dakin taron majalisar zartarwar jihar ranar Alhamis a Gusau.

Sabababbin ma’aikatun da aka amince da su sun haÉ—a da ma’aikatar:

  • Noma
  • Kasafin kudi da tsare-tsare
  • Kimiyya da Fasaha
  • Muhalli da Arzikin Æ™asa
  • Kudi
  • Lafiya
  • Kasuwanci
  • Cikiniki da Masana’antu
  • Gidaje da Bunkasa Birane
  • Shari’a
  • Al’adu da Yada Labarai
  • Kananan Hukumomi da Masarautu
  • Addinai
  • Mata da Cigaban Jama’a
  • Matasa da Wasanni
  • Aiyuka da Ababen more rayuwa
  • Tsaro da Harkokin Cikin Gida

More News

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naÉ—a

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...