
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya nemi afuwar mutanen Taraba h waɗanda ya batawa a tsawon wa’adinsa na shekara 8.
Ishaku ya nemi ayi masa afuwa ne yayin taron addu’ar nuna godiya da kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Taraba ta shirya a hedkwatar ta dake Jalingo.
Gwamnan ya ce yayi murna cewa takensa na ” Ku bani Zaman Lafiya Ni Kuma Zan Kawo Muku Ayyukan Cigaba.” ya samu wurin zama a zukatan al’ummar jihar.
Tun da farko Ishaku a wurin taron addu’o’in Bikin Ista na musamman da aka gudanar a Cocin Anglican dake Mayo Dosa a Jalingo ya durkusa har ƙasa a gaban mahalarta taron inda ya nemi gafarar mutanen da ya batawa a cikin shekaru 8 na mulkinsa.
Za a iya cewa Gwamna Ishaku ya bi sawun shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da suka nemi jama’a su ya fesu