
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya sasanta rikicin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Suru da Koke Besse na jihar domin kawo zaman lafiya.
Ya ce tattaunawa ita ce sahiyiyar hanya ɗaya ta magance rikicin manoma da makiyaya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Idris wanda ya garzaya zuwa yankin biyo bayan rikicin manoma da makiyaya da aka yi asarar rayuka biyu a yayin da aka kwantar da wasu takwas a asibiti biyo bayan raunin da suka samu.
Ya bayar da tallafin miliyan 4 ga waɗanda suka mutu a yayin da wadanda suka jikkata aka basu tallafin miliyan biyar a karamar hukumar Suru.
A yayin da yake karamar hukumar Besse inda mutane biyu suka ɓata aka kuma kashe mutum ɗaya gwamnan ya gaggauta kwamitin sasantawa ƙarkashin jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar da kuma sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka haɗa da DSS da kuma Civil Defence.