Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishinan da ake zargi da lalata da matar aure

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya dakatar da Auwal  Danladi Sankara kwamishinan ayyuka na musamman na jihar kan zargin da ake masa na lalata da matar aure.

A ranar Juma’a ne hukumar Hisba ta jihar Kano ta sanar da kama Sankara a cikin wani gida da ba a kammala ba tare da wata matar aure inda hukumar ta zarge shi da aikata baÉ—ala.

A wata sanarwa ranar Asabar, sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ya ce an dakatar da kwamishinan har sai an kammala binciken laifin  da ake zarginsa da aikatawa.

Sanarwar ta ce an É—auki matakin ne a matsayin kariya domin gudanar da cikakken bincike.

“Mun É—auki dukkanin zarge-zarge da muhimmanci kuma mun bada muhimmanci wajen tabbatar da yardar da mutanen Jigawa suka yi wa gwamnati,” ya ce.

Sai dai kwamishinan ya musalta zargin da ake masa kuma ya ci alwashin gurfanar da hukumar ta Hisba a gaban kotu.

More News

An kashe shugaban wata makaranta a Abuja a cikin gidansa

Wasu mutane da kawo yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe, Bala Tsoho Musa shugaban makarantar Abuja Rehabilitation Centre. Musa wanda aka...

APC ta lashe zaben kujerun ƙananan hukumomi da kansilolin jihar Kaduna

Jam'iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kaduna 23 da kuma na kejerun kansilolin jihar. Hajara Muhammad shugabar hukumar zaɓe mai zaman...

Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Birtaniya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan da ya shafe mako biyu yana hutu a Birtaniya. Shugaban ƙasar ya sauka a filin...

An sallami Æ´an sanda uku daga bakin aiki kan kisan wani dalibi

Rundunar Æ´an sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami'an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya...