
Hakkin mallakar hoto
Tun bayan da gwamnan jihar Borno farfesa Umar Babagana Zulum, ya yi kakkausar suka dangane da abin da ya kira ‘karbar na goro’ da sojojin Najeriya ke yi a shingayen da suke kafawa a manyan titunan fadin jihar, jama’a ke ta fadin albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta.
Gwamnan dai ya kai wata ziyarar bazata ne ga wani shingen da sojoji suka kafa da ke kan babbar hanya a garin Jimtilo.
An dai ce gwamna Zulum da kansa ya ba da hannu ga cincirindon motocin da suka yi cirko-cirko a kan titin na Jimtilo, inda mutane suka yi ta yada wa a kafafen sada zumunta kamar haka:
Martanin Sojoji
To sai dai jim kadan bayan kalaman na gwamna Zulum, mai magana da yawun ayyukan rundunar, Kanar Aminu Ilyasu ya mayar da martani, inda ya nuna rashin jin dadin rundunar dangane da kalaman gwamnan.
A sanarwar da Kanar Aminu ya sanya wa hannu ya ce ” fitowar irin wannan zargi daga bakin mutum mai girma kamar gwamna ba komai zai ta haifar ba illa mayar da hannun agogo baya.”
Duk da cewa rundunar sojojin ta ce za ta binciki zarge-zargen ‘karbar hanci’ amma Kanar Aminu ya ce “sojoji mutane ne masu bin ka’idojin aikinsu.”
Sanarwar ta kuma kara da yin kira ga jama’a da su kwarmata duk wani abu da suka ga sojojin na yi wanda bai dace ba.
Gwamnan Borno ya yaba wa Burutai
Shan alwashin yin bincike dangane da halayyar sojojin ta ‘karbar na goro’ da rundunar sojin kasar ta yi, ya sa gwamna Umara Zulum jinjina wa sojojin.
Farfesa Zulum a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Isa Gusau, ya ce hakan na nuna irin kokarin Hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Burutai na dawo wa da rundunar martabarsu.
Sanarwar ta ce ” shawarar daukar matakin bincike na gaggawa kan halayyar sojoji a Njimtilo na nuni da irin aniyar Laftanar Janar Tukur Burutai da kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole da wasu sojoji ta ganin an kawar da rashin zaman lafiya a jihar Borno da yankunanta.”
Wannan dai kusan shi ne karon farko a baya-bayan nan da wani babban jami’in gwamnati ya zargi sojojin kasar da ‘karbar na goro.
An sha samun yanayin da mutane kan yi irin wannan zargin amma jami’an tsaron su karyata.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne sakamakon bincike da rundunar sojin ta ce za ta yi domin daukar matakin shawo kan wannan matsalar.