
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bawa kowane mahajjacin jihar su 3000 kyautar kudi riyal 300.
Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bawa gwamnan shawara kan yada labarai, Alhaji Mukhtar Gidado ya fitar a Bauchi ranar Juma’a.
Gidado ya ce gwamnan ya fadi haka ne lokacin da ya kai ziyara masaukin alhazan jihar dake kasa mai tsarki domin ganawa da su.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Riyal 300 ya kama naira dubu saba’in da biyar kenan.
Gwamnan ya kumagodewa alhazan kan yadda suka nuna da’a a yayin zaman su Saudiya.