Gwamnatin tarayya ta cire manyan makarantu daga tsarin haɗin gwiwar ma’aikata da tsarin biyan albashi na IPPIS.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai fadar shugaban kasa bayani tare da wasu ministoci kan sakamakon taron na FEC.
Sannan ya ce hakan zai fara aiki ne cikin gaggawa.
A cewarsa, FEC ta yi la’akari da cewa shugaban jami’o’in ba sa bukatar su bar aikinsu don zuwa Abuja don neman biyan albashin ma’aikatansu.