GSS Kagara: Wani ɗalibi da ya tsira ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru

Maharan sun shafe kusan awanni uku kafin su fice daga makarantar tare da ɗaliban da suka sata

Bayanan hoto,
Ɗaya daga cikin ɗakunan kwana ɗaliban da aka sace

Da sanyin safiyar ranar Talata ne wasu ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 50, da kuma wani malaminsu da iyalinsa shida mata da ‘ya’ya, a makarantar sakandiren garin Kagara da ke jihar Neja a arewacin Najeriya.

Dangane da wannan al’amari BBC ta tattauna da wani ɗalibi da ya tsira, duk da a gabansa suka kashe abokinsa, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suka sace.

Ya ce kimanin ƙarfe 2 na tsakar daren ranar ta Talata wani daga cikin abokansa ya tashi domin yin fitsari, sai ya lura da wasu mutane na dosowa makarantarsu ta baya riƙe da fitulu suna haskawa.

“A lokacin ne sai abokin nawa ya tashe ni yake ce min ga wasu mutane can suna nufo mu ta bayan makaranta, bai san ko su wanene ba, mu fita mu gani, sai nace masa a’a, kada ya ji tsoro ya koma ya kwanta, sai ya ƙi, ya ɗauki fitila ya haska musu, da suka ga an haska su sai suka yi sauri suka kashe nasu fitilun” a cewar ɗalibin da muka sakaye sunansa.

Ya ƙara da cewa “har lokacin da suka shigo bamu san ɓarayin mutane bane, sai suka ka fara tayar da dalibai daga barci suna ɗora musu bindiga, suna cewa duk wanda ya yi motsi ko ihu za su kashe shi nan take, to a lokacin ne wani ɗalibi ya lura miyagu ne, sai ya ƙwalla ihu ya ce kowa ya gudu ɓarayi sun shigo, abin da ya sa mutane suka fara fita suna ta guduwa.”

”Wani abokina ma munyi sallama da shi zai je ya kwanta, ya tafi kenan ya yi karo da su, juyowar da zai yi zai tsallaka taga ya gudu, sai suka buɗe masa wuta tare da yi masa harbi uku, ɗaya a kansa, ɗaya a baya ɗaya kuma a ciki, har sai da kwanyar kansa ta zazzago waje” inji shi.

Shi dai wannan ɗalibi ya ce ya ɓuya ne tare da wasu abokansa su 10 a wani lungu a wurin kwanan su, wanda hankalin ƴan bindigar bai kai wajen ba, duk da sun riƙa zazzagayawa ta wajen suna duba ko akwai mutane.

”Abun da ya bani tausayi ya kuma bani haushi shine yadda a gabana aka kashe abokina, ga gawarsa a gabana ina kallo, na yi kukan baƙin ciki, iyayena suna ta cewa in yi haƙuri’ a cewar wannan ɗalibi.

Ya ce maharan sun shiga makarantar ne sanye da kayan sojoji dukkaninsu, kuma sun shafe kusan awa uku kafin su tafi da mutanen da yawansu ya kai aƙalla 50, da wani malami guda ɗaya, da iyalan shi mutum shida.

Ko da BBC ta tambaye shi ko a kan me maharan suka zo?, sai ya ce basu zo da babur ko ɗaya ba, da ƙafa suka tako tun daga nesa, sannan ko da suka kwashe ɗaliban a ƙafa suka juya suka tafi da su.

Bayanan hoto,
Kawo yanzu jami’an tsaro sun ce suna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban da aka sace

Zuwa yanzu dai wata tawagar gwamnatin tarrayya daga Abuja da ministan ma’aikatar kula da watsa labarai ke jagorenta ta kai wata ziyara a jihar ta Neja domin tattauna hanyoyin da za bi a samu ceto waɗannan ɗalibai da malaminsu da ‘ya ‘yan shi guda 6 da kuma matar shi da ke hannun waɗanan ‘yan bindiga.

Haka ma ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun gabatar da wani ƙuduri, da ke kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta ayyana dokar ta-ɓaci a bangaren tsaro, ta yadda gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kan matsalar domin magance ta.

Wasu rahotanni sun ce shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya jagorenci wani taron gaggawa a daren ranar Alhamis da wasu gwamnonin jihohin arewacin ƙasar, sai dai babu wasu bayanai dangane da abubuwan da aka tattauna, amma ana kyautata zaton cewa matsalar tsaron na kan gaba.

Wasu masana kan lamuren tsaro dai ga ganin cewa da alama mahukuntan Najeriya basu ɗauki wani darasi daga abubuwan da suka faru a baya, na sace ɗalibai a wasu makarantu da ke arewacin ƙasar ba.

(BBC Hausa)

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...