Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci, Abdullahi Adamu tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa.
Tun bayan da Abdullahi Adamu da sakataren jam’iyar APC na kasa Iyiola Omisore suka ajiye mukamansu ake rade-radin cewa Ganduje zai maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban jam’iyar.
Wata majiya dake kusa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa tuni shugaban kasar ya nuna goyon bayansa ga yunkurin dora,Ganduje a matsayin shugaban jam’iyar.