
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sabon shugaban jam’iyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci zaman taron shugabannin jam’iyar na farko.
Taron ya gudana ne a ofishin jam’iyar na kasa dake Abuja.
A ranar 3 ga watan Agusta ne aka zabi, Ganduje a matsayin sabon shugaban jam’iyar a wurin taron kwamitin zartarwar jam’iyar.
Ganduje ya maye gurbin, Abdullahi Adamu wanda ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin jam’iyar a cikin watan Yuli.