
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da kuma shugaban jam’iyar APC, Abdullahi Umar Ganduje sun fara wani yunkuri na sasanta tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da kuma gwamna mai ci, Hope Uzodimma.
Mutanen biyu sun dade basa ga maciji da juna kan siyasar jihar.
A shekarar 2021 Uzodimma ya nemi umarnin kotu na kwace wasu kadarori mallakin Okorocha.
Ana ganin kokarin shirin nasu na da nasaba da zaɓen gwamnan jihar da za gudanar a cikin watan Nuwamba.