Furucin Sarki Sanusi ya janyo takaddama

Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi na biyu

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Takaddamar da ta kunno kai tun bayan da aka bayar da sanarwar gano wadansu yara da ake zargin sace su aka yi daga birnin Kano na arewacin Najeriya ta ci gaba da ruruwa.

A baya-bayan nan dai wasu kalamai da Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya furta ne suka haddasa ce-ce-ku-ce.

Yayin wani jawabi da ya yi a wajen wani taro a birnin na Kano, Sarki Sanusi ya ce, “Duk yaran nan da ake cewa an sace, kuma ana cewa Sarki bai yi magana ba, mun riga mun yi bayani—tun da aka fara maganar yaran nan na Onitsha, muka yi magana da Obi of Onitsha, kuma muna sane da halin da ake ciki kuma da binciken da ake yi”.

Daga nan ne Sarkin ya ce idan bera na da sata, to daddawa ma na da wari:

“Amma kafin a zo kan wadanda aka ce sun sace mana yara—duk ana ta zage-zage, sun sace mana yara—mun ji, sun yi laifi. Amma shin wanda ya saci yaron nan cikin gidanka ya shigo ya sace shi? Ko kai ne ka bar danka dan shekara uku ya fita yana yawo a kan titi ba ka ma san inda yake ba?

“Ni na fada—na san sanda aka kama wasu aka kawo kara gaban Sarki—a lokacin cewa na yi da ni nake da gwamnati, da duk mahaifansu sai na daure su.

“Kuma har na ce a nemi kwamishinan ‘yan sanda, shin ba mu da doka ne da ake cewa criminal negligence? …Laifi a wajenmu yake, mu ne masu laifi.”

Martanin Sarki

Sarkin ya yi wadannan kalaman ne dai bayan ce-ce-ku-ce da aka yi ta yi a Kano, game da rashin jin martaninsa kan batun.

A karshen watan Oktoba ne rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce ta ceto wasu yara tara waÉ—anda ta ce wasu ‘yan kudancin Æ™asar ne suka sace suka kuma sayar da su a jihar Anambra, tare da sauya musu suna da addini.

  • ‘Sayyadina Umar ya taba aika sako Daular Borno’
  • ‘Hukuncin kisa ga duk wanda ya saci yaro’

Kalaman Sarkin dai sun janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman ma Kano inda wasu ke cewa abin da Sarkin ya fada gaskiya ne yayin da kuma wasu ke cewa har cikin gida aka shiga aka É—auki É—aya daga cikin yaran.

Hidaya Salisu Ahmad ta goyi bayan kalaman Sarkin inda ta ce “Gaskiya wannan maganar ta yi daidai saboda za ka ga idan iyaye suna hayaniya sai a ce wa yaro jeka waje ka yi wasa kuma shekarunsu bai kai su fita su kadai ba.”

“A tunanna, a ce wai wannan laifin iyaye ne, wannan kuskure ne saboda wani ya tura É—ansa makaranta amma an dauke shi,” in ji wani magidanci a Kano.

A ranara 31 ga watan Octoba gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin jin bahasi kan sace yaran bisa karkashin jagorancin Mai Shari’a Wada Umar Rano.

Tuni kwamitin ya fara zamansa a kotun da ke Miller Road, bayan kira ga iyayen yaran da kuma masu ruwa da tsaki domin gabatar da bayanai.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...