Farashin iskar gas ya sauko a Najeriya

Wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa matsakaicin farashin iskar gas din girki a Najeriya ya yi sauko zuwa mafi karanci farashi cikin watanni hudu da suka gabata.

A cewar dillalan kasuwar, an samu raguwar farashin ne saboda hada-hadar ayyukan gwamnati da suka hada da cire harajin (VAT) da harajin shigo da gas na dafa abinci domin bunkasa kayan cikin gida da kuma daidaiton darajar Naira da  dala a kasuwar canji.

Har ila yau, gwamnati ta fara rarraba silindar LPG miliyan ɗaya kyauta a duk faɗin ƙasar don haɓaka hanyoyin shiga.

Binciken kasuwa ya nuna cewa farashin iskar gas a halin yanzu ya fadi kasa da ₦900 kan ko wacce kilogiram a karon farko cikin watanni hudu.

More from this stream

Recomended