EU zata tattauna kan sabuwar dokar kasar Hungary | Labarai

A cewar wani jami’in kungiyar, batun cecekuce kan sabuwar dokar kasar Hangary din wani babban abun dubawa ne a taron da zai gudana a ranakun Alhamis da Juma’a. Batun dai na zama na gaba-gaba a siyasar Turai a wannan makon biyo bayan matakin Hukumar Kwallon Kafa ta Turai na haramta shirin haskaka filin wasan Munich cikin launukan da ke alamta auren jinsi yayin wasa tsakanin Jamus da kasar Hungary a ranar Laraba.

Fiye da rabin kasashen dake kungiyar ta EU da suka hada da Jamus da Faransa da Italiya da kuma Spaniya ne suka yi wa kasar ta Hungary rubdugu kan sabuwar dokar tare da yin kira kungiyar ta dau mataki da a ganinsu take hakkin ne.

Kazalika kuma ana ganin cewa wannan taron ka iya zama na karshe da shugabar gwamnatin Jamus zata halarta a matsayinta ta shugaba a kungiyar ta EU.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...