Emefiele ya isa kotun da ake tuhumarsa a Legas

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele, ya isa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas, bisa tuhumarsa da laifuka biyu da suka hada da mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kawo shi da karfe 09:21 na safe.

An gurfanar da Emefiele a gaban alkalin, Justice Nicholas Oweibo.

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Joseph Daudu, shi ne ya jagoranci sauran lauyoyin da ke kare Emefiele.

Shugaban bankin da aka dakatar bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

More News

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...