Emefiele: An Samu Yamutsi Tsakanin Jami’an DSS dana Hukumar Gidan Yari

An samu yamutsi a harabar babbar kotun tarayya dake Ikoyi a jihar Lagos bayan da jami’an tsaron DSS suka yi kokarin kwace, Godwin Emefiele tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN daga hannun jami’an hukumar gidan yari ta Najeriya.

A ranar Talata ne aka gurfanar da Emefiele a gaban kotun tun bayan da aka tsare shi a watan Yuni.

Mai shari’a, Nicholas Oweibo ya bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin kan kudi naira miliyan 20.

Sauran sharudan sun hada da kawo mutum guda wanda yake da kadara a yankin Ikoyi, mika fasfonsa na tafiye-tafiye da kuma kawo ma’aikacin gwamnati dake matakin albashi na 16.

Alkalin ya yi umarnin a tasa keyar Emefiele zuwa gidan yari har sai ya cika sharudan belin.

Amma mai makon a mika shi ga jami’an gidan yari, jami’an tsaron DSS sun yi kokarin yin gaba da shi yunkurin da ya gamu da turjiya daga jami’an gidan yarin.

A gumurzun da aka yi ta kai ga an yaga rigar wani jami’in gidan yarin.

A karshe dai jami’an na DSS saboda yawansu sun samu nasarar tafiya da Emefiele.

More from this stream

Recomended