EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Buhari Da Zargin Laifin Satar Naira Biliyan 22

Hukumar EFCC dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta tsare tsohon ministan wutar lantarki, Sale Mamman kan zargin sa da karkatar da kuÉ—in da yawansu ya kai biliyan 22.

Mamman ya rike muƙamin ministan wutar lantarki daga shekarar 2019 zuwa 2021 lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauke shi daga kan muƙamin sa.

An tsare shi ne bayan da ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa zuwa ofishin ta dake Abuja.

Wasu majiyoyi a hukumar EFCC sun bayyana cewa Mamman ya haÉ—a baki tare da wasu ma’aikatan ma’aikatar wutar lantarki inda suka karkatar da naira biliyan 22 suka kuma raba su a tsakaninsu.

More News

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Kotu ta bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wato KANSIEC da ta cigaba da shirye-shiryen gudanar da...

Ministan tsaro Badaru ya yaba wa gwamnan Zamfara saboda tallafa wa aikin soji a jihar

Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji a Jihar Zamfara.Ministan...