EFCC ta kama masu sayen kuri’a a zaben gwamna

EFCC ta ce ta cafke mutum 14 a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi bisa zargin su da yunƙurin sayen ƙuri’u daga masu zaɓe a zaɓen gwamnonin jihohin da ya gudana a ranar Asabar.

Hukumar ta ƙwace kuɗi naira miliyan 11,040,000 daga irin waɗannan mutanen.

An kama waɗanda ake zargin ne a garin Otueke da Adawari na jihar Bayelsa, da kuma wasu a jihohin Kogi da Imo.

EFCC ta ce ta samu nasarar hakan ne sanadiyyar bayanan sirri da ta tattara tun gabanin ranar gudanar da zaɓukan.

Bugu da ƙari hukumar ta samu nasarar ƙwace motoci biyu daga masu ƙoƙarin aikata laifukan na zaɓe.

Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala gudanar da bincike a kansu.

A wannan Asabar ɗin ne INEC ta gudanar da zaɓukan gwamnan a jihohin na Kogi da Imo da Bayelsa, zaɓukan da aka samu koke-koke na tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankuna daban-daban.

More from this stream

Recomended