
Jami’an hukumar EFCC sun samu nasarar kama wasu makudan kudade da suka kai naira miliyan 32 da ake zargin an yi shirin sayan kuri’a da su.
A cikin wata sanarwa da ta fitar hukumar EFCC ta bayyana cewa an kama kuɗin ne a jihar Lagos.
Jami’an hukumar ne dake jihar ta Lagos suka samu nasarar kama kuɗaɗen.
Kamen na zuwa ne a ƙoƙarin da hukumar take na yaƙi da sayan kuri’a a zaɓuka masu zuwa.