ECOWAS ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai kan sojojin Nijar

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta yi Allah wadai da kisan da wasu kungiyoyi dauke da makamai suka yi wa sojojin Nijar.

Sojojin Nijar 17 ne aka kashe a ranar Talata a wani hari da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai a kusa da iyakar kasar da Mali da ke yammacin kasar, in ji ma’aikatar tsaron kasar.

Wani sashen sojojin ne “harin ta’addanci ya rutsa da shi a kusa da garin Koutougu,” in ji ma’aikatar cikin wata sanarwa da yammacin Talata.

Ya kara da cewa wasu sojoji 20 sun jikkata, shida masu tsanani, sannan an kwashe dukkan wadanda suka jikkata zuwa Yamai babban birnin kasar.

Sama da maharan 100 ne aka É“atar da su, in ji rundunar.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ECOWAS ta nuna damuwa kan kashe-kashen da aka yi wa sojoji a Nijar, yayin da ta nuna juyayi ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Sanarwar ta kara da cewa, “ECOWAS ta samu mummunan labarin bakin ciki na hare-hare daban-daban da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai a Jamhuriyar Nijar wadanda suka yi sanadin mutuwar sojojin Nijar da dama.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...