DSS ta kama jami’ai masu karkatar da kayan tallafin da za a ba wa talakawa

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), a ranar Talata, sun kama wasu jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar da ke karkatar da kayayyakin tallafin jama’a da ake yi wa ‘yan kasa don dakile raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin da aka kama a wata shahararriyar kasuwa da ke garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa inda ake sayar da kayayyakin sun hada da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Nasarawa (NASEMA) da sauran abokan aikinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan sirri, Peter Afunanya, wanda ya bayyana wa manema labarai ci labarin a Abuja, ya bayyana cewa an kwato wasu daga cikin kayayyakin da aka karkatar daga hannun wadanda ake zargin.

Afunanya ya yi kira ga jama’a da ke da bayanan da suka shafi al’amuran da suka kunno kai da su kai rahoto ga jami’an tsaro da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace, yana mai cewa za a hukunta masu laifin kamar yadda doka ta tanada.

“Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu rahotanni daga wasu Gwamnonin Jihohin da suka shafi karkata ko sayar da kayan abinci da ake da niyyar ba wa ‘yan kasa.

“Saboda haka, hukumar ta gudanar da bincike a kan haka kuma ta gano wasu daga cikin kayayyakin tare da kama wadanda ake zargin,” in ji kakakin DSS.

Ya kara da cewa yayin da suke ci gaba da gudanar da ayyukansu a wasu jihohin, tuni hukumar ta kama wani da ake zargi da aikata laifuka a jihar Nasarawa da ke da hannu wajen karkatar da kayan abinci da kuma sayar da kayan agajin da aka tanadar wa masu karamin karfi a wurin.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...