Dimokradiyya: Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin 12 ga wata a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 12 ga watan Yunin 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta bana.

Dokta Oluwatoyin Akinlade ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya daukacin ‘yan Nijeriya murnar wannan rana.

“Tafiyar Dimokuradiyyar Najeriya, kamar a sauran yanayi da dama, ta ci karo da kalubale, amma shugabannin kasa, da cibiyoyinta da ma al’ummar Nijeriya, sun tsaya tsayin daka kan tsarin mulkin dimokradiyya.

“Saboda haka, a wannan karon, an gayyaci ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya, da su yaba irin ci gaban da aka samu, da nuna farin cikinsu, da kuma fatan samun kyakkyawar makoma ga dimokuradiyyar kasar nan,” inji shi.

More from this stream

Recomended