DCP Tunji Disu: Wane ne Tunji Disu da ya gaji Abba Kyari?

Tunji Disu

Asalin hoton, Other

A ranar Litinin ne Babban sufeto janar na Æ´an sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya amince da naÉ—in DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).

Wannan na nufin ya maye gurbin É—an sanda nan Abba Kyari da aka dakatar kan zargin rashawa.

Sanarwar da ke dauke da sa hannun jami’in yaÉ—a labaran rundunar, CP Frank Mba ta ce DCP Disu zai kama aiki gadan-gadan ba tare da É“ata lokaci ba.

Kuma a cewar sanarwar IGP Alkali na sa ran sabon shugaban ya nuna ƙwarewa da jagoranci wajen aikawatar da aikinsa da sauke nauyin da aka dora masa.

Sannan ya tabbatarwa ƴan kasa cewa wannan sashi na IRT zai ci gaba da aiki tuƙuru wajen kare kasa da manufofinta daga ɓata gari.

An haifi Tunji Disu ranar 17 ga watan Afrilun 1960 a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Kafin naÉ—in DCP Disu wannan mukamin, shi ne tsohon kwamandan kai agajin gaggawa na Rapid Response Squad (RRS) ta jihar Legas.

Ya kuma riƙe muƙamin mataimakin kwamishina a sashin ayyuka na rundunar a hedikwatarta ta Abuja.

An ƙara masa muƙami daga mataimakin kwamishinan ƴan sanda ASP zuwa mukaddashin kwamishinan ƴan sanda DCP a watan Afrilun 2019.

Mista Disu ya yi aiki a matsayin kwamandan kai agajin gaggawa na Rapid Response Squad (RRS) daga shekarar 2015 zuwa 2020.

Sannan ya yi aiki a sashen leƙen asiri na CID a jihar Ribas a matsayin mataimakin shugaban sashen.

Disu ne tsohon kwamandan rundunar ƴan sandan Najeriya a Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka a Dafur, da ke Sudan.

Mista Disu yana da digiri a Ingilishi daga Jam’iar jihar Legas (LASU).

Sannan ya yi digirinsa na biyu a kan Sha’anin Mulki daga Jami’ar Adekunle Ajasin University daga jihar Ondo.

Ya halarci horo a kan wasu kwasa-kwasai na neman ƙwarewa a Najeriya da ƙasashen waje kamar:

  • Fasa Æ™wabrin Æ™ananan makamai a Botswana
  • Horo kan Æ™warewa a hana zamba ta intanet a Jami’ar Cambridge ta Birtaniya
  • Horon Æ™warewa kan sanin makamar shugabanci a Kwalejin Ƴan sanda ta Jos
  • Binciken kimiyya na gano masu aikata laifuka da na leÆ™en asiri kan masu aikata muggan alifuka a Jami’ar Legas
  • Kazalika Disu mamba ne na Ƙungiyar Shugabannin Ƴan sanda ta Najeriya, da Cibiyar HulÉ—a da Jama’a da kuma Cibiyar Nazarin Harkokin Jama’a.

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...