Darajar kuɗin Naira na cigaba da faɗuwa a kasuwar musayar kuɗade

Darajar takardar kudin naira tayi faduwar da bata taba yi ba a kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage inda ake canza dalar Amurka kan naira 1170.

Takardar kuɗin ta Najeriya ta yi kasa da N105 ko kuwa kaso 9.8 cikin ɗari idan aka kwatanta da yadda aka canza ta kan kuɗi N1065 a ranar Laraba.

A cewar wasu yan canjin kuɗi dake unguwar FESTAC a jihar Lagos darajar naira ta faɗi ne sakamakon ƙarancin dalar Amurka da ake fuskanta.

Yan kasuwar canjin kudaden sun ce suna sayan dalar Amurka akan naira N1155 su kuma su sayar kan 1170 ribar naira 15 kenan.

Amma kuma darajar ta naira ta yi sama kaɗan a kasuwar hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna inda ake canza dalar Amurka ɗaya kan N790.68 mai makon naira 848 da aka rika sayar da kowace dala a ranar Talata.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...