
Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jos South and Jos North, Dachung Musa Bagos ya shawarci mutanen mazabar sa da su yi amfani da damar da kudin tsarin mulki ya basu ta kare kansu.
Bagos ya bayyana haka ne lokacin da yake mayar da martani kan kashe kashen dake faruwa a Mangu da kuma Jos South.
Sama da mutane 20 aka ba da rahoton an kashe a harin da wasu yan bindiga suka kai a ranar Lahadi.
Bagos wanda ya bayyana damuwars kan hare-haren ba tare kakkautawa ba ya shawarci mutanen su kare kansu kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya basu.
Dan majalisar ya koka cewa yawancin mutanen mazabarsa suna zaune cikin zullumi ya kara da cewa kusan kullum sai an kai hari.