Dan gidan wani boka ya mutu a lokacin gwajin maganin harbin bindiga

An harbe Tunde Akinmoyewa mai shekaru 27 har lahira ɗa ga wani mai maganin gargajiya a sansanin Laoso dake Laje a karamar hukumar Ondo West ta jihar Ondo.

Abokan Tunde ne suka harbe shi har lahira a lokacin da suke kokarin gwada maganin bindiga da wani boka ya basu a sansanin.

Marigayin wanda a baya ya taba zaman gidan yari an ce ya sha hade-haden maganin ne da aka ce yana kawar da harsashin bindiga daga taba jikin mutum da aka hada musu shi da mutanensa domin ya tabbatar da ingancinsa.

Tun da farko bokan ya tabbatarwa su Tunde cewa babu wani harsashi da zai ratsa su matukar suka sha maganin.

A cewar wata majiya a kokarin gwada karfin maganin ne Tunde ya umarci abokinsa da ya harbe shi inda ya mutu nan take.

More from this stream

Recomended