Cututtukan da auren zumunci ke jawowa

Mace ta lullube fuska

Auren zumunci ko na dangi ba sabon abu ba ne tsakanin ƙabilu, inda wasu ƙabilun suke bayar da matuƙar muhimmanci a kansa domin inganta dangantakar da ke tsakaninsu.

Sai dai duk da auren zumunci da ake yi tsakanin Æ´ar wa da É—an Æ™ane, da kuma makamantansu yana da fa’idoji ta É“angaren zamantakewa da kuma Æ™ara danÆ™on zumunci, a kimiyance ta É“angaren lafiya, likitoci sun ce yana da haÉ—ari.

Dr Ibrahim Musa, masanin lafiyar jini a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano a arewacin Najeriya ya ce auren zumunci yana haifar da ƙarin yiwuwar samun cututtukan da ake gada daga iyaye.

Misali, kamar ciwon sikila wanda iyaye sukan kasance suna da nau’in wannan ciwon tare da su, idan aka ci gaba da auratayya ciwon zai ci gaba da yaÉ—uwa.

Sannan masanin ya ce akwai cututtuka da na gado wanÉ—anda auren zumunci ke haifarwa ba tare iyali sun sani ba.

Ƙwayar halittar dangi

Mujallar Lafiya ta The Lancet a 2013, ta ce Æ™wayoyin halittar ma’aurata na iya shafar kowaÉ—anne ma’aurata, komai asalinsu ko Æ™abilarsu.

Misali wadda ta auri É—an uwanta da suke jini É—aya za ta fi fuskantar matsala a Æ´aÆ´an da za ta haifa.

Ko da yake a wani cikakken bayani da Hukumar Lafiya ta Ingila NHS ta yi game da matsalar ta ce ba a cika samun matsala ba a yawancin Æ´aÆ´an da aka haifa ta hanyar auren zumunci, yawanci ana haihuwarsu ne da lafiya.

Amma ta ce auren zumunci kamar na ƴar wa da ɗan ƙane ko ƴaƴan wa da ƙanwa, ya fi haifar da matsala ga ƴaƴan da za su haifa da kashi uku zuwa shida, amma kuma matsalar ba mai yawa ba ce.

Ana samu matsala idan ma’auratan biyu sun gaji kwayoyin haliyyar da ke da matsala daga iyayensu.

Me ya sa ƙwayoyin halitta ke da muhimmanci ga dangi

Yan uwa daga dangi ɗaya suna da adadi mafi yawa tsakaninsu na ƙwayoyin halittarsu. Ƙwayoyin halittar kuma ginshiƙi ne da ke sarrafa jiki.

ƙwayoyin halittar ne ke daidaita launin ido da girmansa da girman ƙafafu da hannaye da sauransu.

Ana gadar abubuwa da dama daga iyaye, kamar yadda za mu iya gadar cututtuka da dama daga gare su, ta hanyar ƙwayar halittarsu.

Wannan zai iya shafar al’ummar da dama, amma ya fi yawa tsakanin dangin da ke auratayya tsakaninsu.

Haihuwar Æ´aÆ´a da nakasa

NHS ta ce ana samun matsaloli na gado cikin kowace al’umma a duniya. Kuma al’ummar da ke yin auren zumunci sun fi yawan yaran da ke da matsaloli na gado.

A cewar NHS Æ´an asalin asalin Pakistan a Birtaniya sun fi yin auren zumunci tsakaninsu, kuma tsakaninsu aka fi samun yaran da ake haihuwa da matsaloli na gado.

Matsalar tana faruwa ne idan akwai wata kwayar halitta ta daban a dangi kuma iyayen duka suna da wannan kwayar halittar. Idan a cikin dangin wasu suka auri junansu akwai yiyuwar ƴaƴan da za su haifa su yi gadon wannan ƙwayar halittar daga iyayen biyu.

Dr Ibrahim ya ce tun da cutar tana cikin dangi kuma aka ci gaba da auratayya, ciwon zai ci gaba da yaÉ—uwa daga yayan da aka haifa,”

Sauran cututtukan gado da likita ya bayyana da ake samu ta hanyar auren zumunci sun hada da: Ciwon taɓin hankali da tawaya ta halitta.

A cewar likitan, bincike ya nuna ciwon na gado na haifar da yawan yin É“ari. Haka kuma yakan iya kara cutuka da ake gada kamar yawan zubar da jini.

“Ko a kwanakin baya an gano wasu ma’aurata a Æ™aramar hukumar batsari ta jihar Katsina waÉ—anda suka kasance Æ´aÆ´an maza zur, wato uban matar da uban mijin Hassan ne da Hussaini, sai suka haÉ—a Æ´aÆ´ansu aure.

“To Æ´aÆ´an nasu ne suka dinga haifar Æ´aÆ´a masu tawayar halitta, wato ba su da gurbin idanuwa, sannan wani hancinsa ya kwalmaÉ—e da sauransu.

“To wannan duk ba komai ya jawo ba sai abin da ake kira Fraser II syndrome wato wasu Æ™wayoyin halitta na gado da suke da tawaya da ake samu daga jikin dukkan iyayen biyu da ke da alaÆ™a ta jini,” kamar yadda Dr Musa ya shaida wa BBC.

Kansar ido

Auren zumunci kan iya janyo wata nau’in cuta ta kansar ido, kamar yadda tsohuwar babbar jami’ar shirin taÆ™aita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ta bayyana a wata hira da BBC.

Cutar na fitowa ne a dai-dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya riƙa tuntube kamar yadda likitar ta bayyana.

Likitar ta ce auren zumunci ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadin a haifi yaro mai irin wannan lalurar.

Kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar kamar yadda likitar ta bayyana.

“Irin wannan cuta ta kansar ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar,” in ji ta.

Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarwari cewa samun bayanan likita game da ƙwayar halitta abu ne mai muhimmanci ga dangi.

NHS ta ce Bayanan za su yi amfani ga duk wanda ke da matsala ta gado a danginsa ko kuma waÉ—anda ke da irin wannan damuwar.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...