Cutar Anthrax:Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi Akan Cin Ganda

Gwamnatin tarayya ta fitar da wani gargadi kan barkewar cutar anthrax a wasu daga cikin kasashe makota da kuma cin ganda.

A wata sanarwa ranar Litinin,Ernest Umakhihe babban sakataren ma’aikatar gona ya ce cutar ta halaka rayukan mutane a arewacin Ghana dake da iyaka da Togo da Burkina Faso.

Cutar Anthrax wata cuta ce nau’in Bacteria dake kama dabbobi masu cin ciyawa irin su shanu, akuya da kuma tinkiya.

Mutane za su iya kamuwa da cutar idan suka yi mu’amala da dabbobi masu É—auke da ita ko kuma naman dabbobin.

Amma kuma cutar ta Anthrax bata yaÉ—uwa daga mutum zuwa mutum.

Alamomin cutar sun haɗa da tari, zazzaɓi da kuma ciwon jiki rashin ganowa tare da yin maganinta ka iya kai wa ga mutuwa.

Umakhihe ya ce dabbobin da ba a yi musu riga-kafi ba kuma suke ɗauke da cutar to kuwa cikin sauki za su iya yaɗawa mutum ta hanyar shakar ƙwayoyin cutar ko cin naman dabbar.

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...