Coronavirus za ta sa ‘yan uwa su rage aikewa danginsu kudi a Afirka

dollar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa za a samu raguwar kudaden da mutane ke aika wa gida daga kasshen duniya da kashi 20 cikin 100 a wannan shekarar, yayin da ake fuskantar matsalar tattalin arziki da kuma rufe harkokin kasuwanci a duniya saboda cutar korona.

Wannan shi ne babban koma bayan da aka fuskanta kan abin da aka kira madogarar rayuwar mutane da dama a Afrika da kuma sauran nahiyoyi.

‘Yan ci rani da yawa ba za su samu damar aikewa da kudade gida ba saboda ayyukansu da kuma abin da ake biyansu na cikin halin rashin tabbas.

Kudaden da ma’aikata daga kasashen waje a duniya ke aikewa gida kasashensu, an yi hasashen za su ragu da kusan dala biliyan 445.

Hasashen ya ce za a samu raguwar ne a kasashen Kudu da Hamadar Sahara da kashi 23 cikin 100 wanda yawan kudin zai kai dala biyan 37 a wannan shekarar.

Ga taswirorin da ke nuna yadda lamarin yake:

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...