Coronavirus: Yadda fiye da mutum 1,000 suka kamu cikin wata daya a Najeriya

Alkalumman cutar Korona a Najeriya

—BBC Hausa

Image caption

Yadda alkalumman cutar korona ke sauyawa a Najeriya

Cutar korona na kara yaduwa a Najeriya inda ake samun karuwar masu dauke da cutar, kuma take kara yaduwa a sassan kasar.

Cikin wata daya an samu mutum fiye da 1,000 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Alkaluman cutar da hukumar NCDC ke fitarwa sun sauya daga 42 da aka bayyana sun kamu a ranar 24 ga Maris zuwa 1,095 a ranar 24 ga Afrilu.

A rana daya 24 ga Afirlu, mutum 114 aka tabbatar da sun kamu da cutar, haka ma a ranar 21 ga Afrilu mutum 117 suka kamu, adadi mafi girma da aka samu a Najeriya.

Sannan yawan wadanda suka mutu cikin wata daya sun haura 30 tsakanin 24 ga Maris zuwa 24 ga Afrilu.

Sai dai yayin da cutar ke kara yaduwa, ana kuma kara samun wadanda ke warkewa daga cutar.

Zuwa yanzu cutar ta yadu a jihohi 26 na Najeriya hadi da Abuja. Kuma yanzu alkalumman hukumar NCDC sun nuna yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai 1,095 yayin da 208 suka warke, 32 kuma suka mutu.

Tarayyar Afirka ta ce adadin mutum 27,862 suka kamu da cutar korona a kasashe mambobinta 52.

Alkalumman da bangaren kungiyar da ke kula da cututtuka masu yaduwa ya wallafa a Twitter sun bayyana cewa cutar korona kawo yanzu ta kashe mutum 1,304 yayin da kuma mutum 7,633 suka warke.

Cutar ta fi yaduwa a yankin arewacin Afirka, kamar yadda alkalumman suka nuna.

An dauki kwanaki 90 kafin cutar ta kashe mutum 100,00 a fadin duniya daga ranar da aka fara samun mutuwa a Wuhan inda aka fara samun bullar korona a China ranar 11 ga watan Janairu.

Cikin kwanaki 16 kuma, yanzu adadin wadanda suka mutu sun zarta 200,000 a duniya

Cutar ta fi yin kisa a Amurka inda aka ruwaito sama da mutum 52,400 sun mutu. Sai kuma Italiya da Spain da Faransa da kuma Birtaniya inda yawan wadanda suka mutu suka zarta 20,000

Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa nahiyar Afirka ka iya zama cibiyar cutar korona saboda yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar a nahiyar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ya kamata Afirka ta tashi tsaye don tunkarar munin halin da za a shiga sakamakon annobar cutar korona tare da shirya yaki da ita.

A cewar Tedros : “Ya kamata nahiyar ta lura da yadda cutar ke saurin yaduwa.”

Shugaban ya yi gargadin cewa duk da kasancewar babu masu fama da cutar sosai a nahiyar, amma ya kamata a dauki matakin da ya dace wajen hana yaduwarta, kafin ta bazu cikin al’umma.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...