Coronavirus: Yadda cutar ta ta’azzara gabar Amurka da China kan Afrika

File photo taken in November 2017 shows US President Donald Trump (R) and Chinese President Xi Jinping attending a welcome ceremony in Beijing

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A yayin da Afirka ke fuskantar samun karuwar masu dauke da cutar korona, su kuwa kasashen Amurka da China kowaccen su na ci gaba da iƙirarin cewa ita ce kan gaba wajen bai wa Afirkar tallafi, sai dai akwai wata a ƙasa da ke ƙara rura wutar gabar fiye da ƙokarin magance cutar, kamar yadda wakilin BBC a Afirka Andrew Harding ya rubuta.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya dage cewa ”babu Æ™asar da za ta iya ja da abin da Amurka ke yi” ta bangaren tallafa wa Afirka kan yaki da cutar korona. Ya kuma ci gaba da cewa ”babu wata kasa da ta taba ko za ta iya yin abin da Amurka ta yi don tallafa wa duniya ta fannin lafiya.

Mista Pompeo yana magana ne a wani taro da ya yi da wata karamar Æ™ungiya ta Afrika da kuma wasu ‘yan jaridar Afrika, kuma wakilin BBC na daya daga cikinsu.

A watan da ya gabata na ɗauki wannan kurari da Trump ke yi cewa babu ƙasar da ke taimaka wa Hukumar Lafiya Ta Duniya kamar yadda Amurka ke yi a matsayin irin kurarin da gwamnatin Trump ta saba yi, wanda kawai yana naɗe tabarmar kunya da hauka ne ta hanyar wanke ƙasar a idon duniya bayan da ta juya baya ga WHO a lokacin da duniya ke cikin matukar halin ka-ka-ni-ka-yi ta fannin lafiya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wadannan yara a Ghana sun tarbi Melania Trump a shekarar 2019. Sai dai ba tare da mijinta ta yi tafiyar ba

Zai zama kamar rashin godiya ne a nuna cewa tallafin da attajirin nan dan kasar China Jack Ma, ya bai wa Afrika daidai yake ko ma ya zarta sabon tallafin dala miliyan 170 da Mista Pompeo yake tunkahon Amurka ta bai wa Afrika.

Sai dai kwanaki kaÉ—an da suka gabata na ga wata maÆ™maÆ™ala a kan Afirka a wata kafar yada labarai ta kasar China, sai hakan ya tuna min kalaman Pompeo, inda har na yi tunanin Afirka ta zama wani sabon fage na yakin cacar bakan Amurka da China – kuma kamar a baya, annobar Covid-19 ce za ta zama abin da fadan zai mayar da hankali kanta.

Nuna adawa da tsarin mulki mai jam’iyyu da dama

Makalar Global Times ta cika baki cewa tsarin siyasar China mai matukar ƙarfi, shi ne ya taimaka wa nasararta ta tunkarar annobar Covid-19.

Daga nan maÆ™alar ta ci gaba. Tabbas yanzu lokaci ya yi da kasashen Afrika za su kawo karshen gwajin da suke yi na kwaikwayon tsarin dimokradiyyar kasashen yamma – gwajin da ya jawo rashin daidaito da rabuwar kawuna kan addini da kabilanci da rikice-rikice da kuma asarar rayuka da dukiyoyi.

A maimakon haka, kamata ya yi Afrika ta bi tsarin mulki mai jam’iyya daya irin na China.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

China ta zuba jari sosai wajen yin manyan ayyuka a Afrika

Jim kadan bayan haka, na sake ganin wata makalar daga wata kafar yada labaran ta gwamnatin China, wacce ta kwarzanta ayyukan da China ke yi na gina tituna a Afrika, wani babban mataki na zuba jari da ayyukan more rayuwa da ke farfado da nahiyar daga shekarun da ta shafe karkashin bauta da mamaya, yanzu kuma ga annobar Covid-19.”

Mista Pompeo ya bayar da amsa a gajarce. Jam’iyyar Gurguzu ta China ta lafta wa kasashen Afirka basussuka kan wasu ka’idoji masu wahala da za su shafi mutanen nahiyar na tsawon lokaci.”

Kwanaki kadan bayan haka na shiga wata tattaunawa ta manhajar Zoom a kan alakar China da Amurka a Afirka – wadda wanda ya shirya taron ya kira ta da alakar wata aba da ke kara tabarbarewa – kuma na saurari wata farfesa ‘yar China da ke cewa cutar korona tana taimaka wa ‘yan jaridar Afrika wajen yaba kyakkyawan tsarin yada labarai na China.

“Kafofin yada labaran kasashen yamma sun fi mayar da hankali kan labarai marasa dadi, masu muni,” a cewar Farfesa Zhang Yanqiu, amma masu karatu sun fi son labarai masu dadi da faranta rai a lokacin da ake cikin tashin hankali.

Ta kuma ce tana son tsarin China na mayar da hankali kan bayar da rahotanni na yadda za a warware matsaloli. Ta ambaci cewa a baya-bayan nan ta ga zakuwar son bin irin wannan tsari daga wajen ‘yan jaridar kasar Habasha.

Amma shin ana iya saurin karkatar da tunanin ‘yan jaridar Afrika?

Na tambayi Mr Pompeo kan ko yana ganin an bata sunan Amurka a idon Afirka sakamakon kalaman Trump na baya-bayan nan kan amfani da maganin wanke datti don magance cutar korona?

Amma sai sakataren harkokin wajen ya ki amsa min tambayar kai tsaye, maimakon haka sai ya ce ba a fahimtar kalaman da Mista Trump ke yawan yi a bainar jama’a, ko kuma wasu kafafen yada labaran da ke adawa da gwamnatinsa kan sauya kalaman nasa.

Fadar hakan ke da wuya sai yawanci mahalarta taron suka nuna yanayin bambarakwai.

Reuters

Listening to Mr Pompeo, it suddenly felt like Beijing and Washington’s views about ‘constructive journalism’ were no longer so far apart”

Amurka ta shafe tsawon shekaru tana amfani da diflomasiyya wajen kare da bunkasa aikin jarida a Afirka daga masu mulkin kama karya da masu hana su fadar albarkacin baki.

Amma a yanzu shugaban Amurka da kansa ya sha karyata ‘yan jaridar kasarsa yana kiran su da masu ”yada labaran karya” kuma ”makiyan al’umma”.

Bayan da na gama saurarar Mista Pompeo, sai kawai na ji cewa China da Amurka ba su da maraba sosai wajen ganin sun inganta harkar yada labarai.

Ba a fahimtar kalaman Trump

A bayyane yake cewa Amurka – tun daga lokacin tsohon shugabanta George Bush ya fitar da wani shirin bayar da agaji da ake kira Pepfar, wanda ya taimaka gaya wajen ciyar da bangaren lafiya gaba a Afirka.

Sannan kuma kowa ya san China tana amfani da annobar Covid-19, da rikicin da Amurka ta samu kanta a ciki a halin yanzu sakamakon annobar, tana tunzura aƙidar siyasarta a nahiyar.

Sai dai hakan ba yana nufin kasashen Afirka ko ‘yan jaridar nahiyar sun zama kwallon da manyan kasashen duniya za su dinga bugawa ba ne a ko yaushe.

Sai dai kuma kasashe nawa ne a nahiyar Afrika da China ke bin su basussukan dumbin kudade sannan kuma a wannan yanayi da tattalin arziki ke fuskantar matsin lamba, watakila za su iya fita daga bin tsarin Amurka su koma bin tsarin China?

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...