Cerezo ya yi takaici kan Cavani; saura kiris Ozil ya bar Arsenal

Edinson Cavani

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Atletico Madrid Enrique Cerezo ya ce ya ji takaicin rashin kawo dan wasan gaban PSG Edinson Cavani dab da rufe kofar kasuwar ‘yan wasa.(ESPN).

Sabon kulob din da tsohon dan wasan Ingila David Beckham ya kafa Inter Miami ya sanar da ci gaba da jajircewa wurin ganin ya kawo Cavani kungiyar.

Shi ma dan wasan gaban Chelsea Tammy Abraham ya ce bai ji dadin gazawar kungiyar wurin sayo dan wasan gaban Uruguay din ba.(Mirror).

Shi kuwa dan wasan Chelsea Willian ya zabi ya tsawaita yarjejeniyarsa da kungiyar a maimakon komawa Barcelona.(ESPN).

A wata mai kama da haka, mai horar da ‘yan wasan Chelsea, Frank Lampard, ya ce yana bukatar kawo mai tsaron raga saboda rashin tabuka abin a-zo-a-gani da Kepa Arrizabalaga ke yi.(Express).

Rahotanni sun ce kadan ya rage Mesut Ozil ya bar Arsenal a ranar karshe ta rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa.(Mirror).

Christiano Ronaldo ya kafa tarihi a matsayin dan wasan Juventus da ya ci wasanni tara a jere a cikin shekara 15.

Liverpool na shirin neman dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho a kaka mai zuwa(Express).

Mai horar da yan wasan Crystal Palace ya shawarci kungiyar da ta fara tunanin yin sabon zubin yan wasa, ganin cewa kungiyar ta kasa shiga kasuwa a watan Janairu.(Telegraph).

Shi kuwa mai horar da ‘yan wasan Lazio Simone Inzaghi ya ce ya so kungiyar ta kawo Olivia Giroud na Chelsea domin kara samun damar lashe kofin Serie A a bana.(Gazetta).

Hakkin mallakar hoto
Reuters

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...