CBN ta ķwace lasisin Heritage Bank

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya kwace lasisin gudanarwa na bankin Heritage.

A wata takarda da bankin ya fitar, ya ce ya ɗauki matakin ne “domin tabbatar da ingantaccen tsarin kudi a ƙasar, kuma ya yi hakan ne a karkashin sashe na 12 na dokar bankuna da sauran harkokin kudi (BOFIA) ta 2020”.

Babban Bankin ya ce soke lasisin ya zama wajibi bayan da bankin na Heritage ya ci gaba da saba wa sashe na 12 (1) na BOFIA 2020 da gazawarsa wajen inganta ayyukansa na kuɗi inda yake haifar da babbar barazana ga daidaiton kuɗi.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa da CBN ya yi da bankin tare da tsara matakan sa ido daban-daban da nufin dakile koma bayan tattalin arziki amma kuma bankin ya ci gaba da taɓarɓarewar kuma ba shi da wata alama ta murmurewa abin da ya sa CBN ya ɗauki matakin soke lasisin a matsayin mataki na gaba.

Hakazalika, CBN ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa ƙwarin gwiwar jama’a kan tsarin banki da kuma tabbatar da cewa ba a tauye tsarin hada-hadar kuɗin jama’a ba.

Yanzu hukumar Inshorar kuɗi ta Najeriya wato NDIC, ta karɓi ragamar gudanar da harkokin bankin na Heritage.

More from this stream

Recomended