Carrie Johnson: Matar firaiministan Birtaniya za ta kai wasu giwaye Afirka ‘don su yi walwala’

Giwaye

Asalin hoton, David Rolfee / The Aspinall Foundation

Bayanan hoto,
Cikin wadanda za a yi tafiyar da su akwai wasu kanana uku da a halin yanzu ke rayuwa a wani rufaffen gandun daji

Kungiyar kare hakkin dabbobi da Carrie Johnson ke jagoranta na shirin kai giwaye 13 nahiyar Afirka, domin farfado da tunaninsu, a wani mataki da aka yi ikirarin shi ne na farko a duniya.

Mai dakin firaiminista Boris Johnson, ita ce jami’ar yada labarai ta cibiyar kula da dabbobi ta The Aspinall Foundation, wadda ke kula da dabbobi gandun daji da ke Kent.

Shugaban Damian Aspinall ya ce an shaida musu za a saka su a keji na musamman sannan a sanya cikin jirgin sama zuwa kasar Kenya.

“Ba sai an tambaya ba wannan gagarumin aiki ne muka Æ™uduri aniyar aikawa,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

Cikin wadanda za a yi tafiyar da su har da wasu kananan giwaye uku da ake ajiye su a gandun dajin da ke kusa da Canterbury.

Asalin hoton, The Aspinall Foundation

Bayanan hoto,
Kungiyar ta ce tuni aka samar da keji na musamman da aka yo daga kasar Afurka ta Kudu domin wannan balaguro

Mista Aspinall ya ce: “Duk da farin cikin da suke ciki a nan Kent, ba nan ne ainihin inda suka tashi ba.”

Ya shaida wa sashen BBC da ke Kent cewa: “Giwaye ba sa walwala idan an turke su, da wuya su haihu, matansu na rayuwa ne a inda ake rayuwar zahiri.

Rabin giwayen da ake tsare da su, sun narka Æ™iba, suna fama da ciwon kafa, da cututtukan da suka shafi fata da kuma cutar damuwa. Amma muna bakin kokarinmu domin inganta rayuwarsu.”

Mista Aspinall ya amince aikin da za su yi mai matukar hadari ne, wanda shi ne irinsa na farko a duniya.

Ya kara da cewa: “Za mu yi kokarin tabbatar da an yi abin cikin kwanciyar hankali, yadda dabbobin ba za su wahala ba.”

Asalin hoton, The Aspinall Foundation

Bayanan hoto,
Su na fatan giwayen za su zauna a sabon wurin zaman na su nan da watanni 12 ma su zuwa.

Ya kara da cewa giwayen, masu nauyin tan 25, za su yi balaguron cikin katon keji da aka inganta shi da abubuwan da suke bukata domin taimakon gaggawa.

“Da zarar sun saba da shige da fice a cikin kejin shi kenan, domin manufar ita ce a sanya su cikin motocin a-kori-kura, daga nan kuma a zuba su a cikin jirgi sai Afirka.”

Mista Aspinall ya ce za a dauki shekara guda kafin giwayen su saba sosai.

A halin yanzu ana duba yiwuwar kai giwaye wurare biyu a Kenya domin gudanar da aikin, wanda kungiyar kare hakkin dabbobin ke cewa shi ne karon farko da ake kokarin sabuntawa wata dabba tunani da inganta walwala.

Ya kara da cewa: “Da zarar sun fita daga nan wurin, za su kasance cikin farin ciki, su yi ta walwala, ga kuma sauran giwaye da za su gani, duniya sabuwa.

“Idan bukatarmu ta biya, hakika za mu yi alfaharin mun yi wani abin kirki a duniya.”

More News

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...