Bukatu huɗu cikin shida da ɓangaren Wike su ka gabatarwa da shugabancin jam’iyar PDP

Da alama dai rikicin da jam’iyar PDP take fama da shi na neman zama gobara daga Kogi biyo bayan kin amincewa da bukatun bangaren gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da shugabannin jam’iyyar su ka yi.

Biyo bayan zaɓen fidda gwani na dan takarar shugaban kasa da kuma zaɓen wanda zai marawa Atiku baya aka fara takun saka tsakanin gwamnan na Rivers da kuma jam’iyar sa ta PDP.

A wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa sakataren jam’iyar, Umar Tsauri ya ce bukata baza su aiwatu ba.


Sanata Tsauri ya ce akwai buƙatu shida da Nyesom Wike ya gabatar amma ya shaida wa BBC guda huɗu da suka haɗa da:


1-Neman a sauke Iyorchia Ayu daga Shugabancin PDP – “ba za a ce ba zai yiwuwa amma yinsa ba dai-dai bane saboda lokaci”.


2-Atiku ya sa hannu cewa zai yi zangon mulki guda wanda a cewar Sanata Tsauri “babu wanda zai rubuta takarda ya ce zangon mulki daya zai yi.”


3-Buƙatar a janye gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai marawa Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.


4-Sannan neman idan an tashi rabon muƙamai a basu (ɓangaren gwamna Wike) na shugaban ƙasa.

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...