Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin 2020 ga majalisa

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Hirar BBC da Alhassan Ado Doguwa kan kasafin kudin 2020

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Alhassana Ado Doguwa

Ranar Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na 2020 ga ‘yan majalisar dokoki.

Shugaban zai gabatar da kasafin kudin ne a zauren majalisar wakilai, inda ‘yan majalisar dattawa za su hadu tare da na wakilan domin sauraren jawabin shugaban.

Zai gabatar da kasafin kudin ne da misalin karfe biyu a agogon Najeriya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da shugaban kasar zai gabatar da daftarin kasafin kudi a kan lokaci.

  • Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin bana

Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sanya bangaren dokoki a cikin sha’anin kasafin kudin tun ma kafin shugaban ya je zauren majalisar.

A cewarsa, shugaban ya amince a sanya kudin yi wa mazabu aiki a kasafin kudin 2020, yana mai cewa ba za a samu matsala wurin amincewa da kasafin kudin a wannan karon ba.

A baya dai an kai ruwa ruwa tsakanin tsoffin majalisun da suka gabata da bangaren shugaban kasar inda aka yi zarge-zargen yin cushe a kasafin kudin 2017.

Tuni dai aka tsaurara tsaro a kewaye da kuma cikin majalisun dokokin na tarayya inda ake jiran isar Shugaba Buhari.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@BashirAhmaad

More from this stream

Recomended