
Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ce dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima ba zai bawa Najeriya kunya ba idan jam’iyar ta ci zaben shekarar 2023.
Buhari ya fadi haka ne a ranar Juma’a lokacin da yake ganawa da wasu jiga-jigan jam’iyar APC a fadar Aso Rock.
Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Atiku Bagudu gwamnan jihar Kebbi da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Idris Wase na daga cikin wadanda suka halarci taron.
A cewar wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar Buhari ya ce tsohon gwamnan jihar Borno ” Ba zai bawa yan Najeriya kunya ba”.
Shugaban kasar ya kuma ya ba musu kan yadda suka taimaka aka yi babban taron jam’iyyar lafiya da kuma zabukan fitar da gwanaye na jam’iyyar.