
Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka 7 a jihar Katsina.
Kaddamar da ayyukan a ranar Asabar na daga cikin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da Buhari yake a Katsina.
Ayyukan da shugaban kasar ya kaddamar sun haɗa da gyaran babban asibitin Katsina, gadar kasa ta Kofar Kaura, aikin gyran tashar turo ruwa,gadar kasa ta Kofar Kwaya da kuma cibiyar karatun ilimin lura da yanayi dake Katsina da kamfanin shinkafa na Darma.




