Buhari da Atiku: PDP ba ta amince da hukuncin kotu ba

Alamar jam'iyyar PDP

Hakkin mallakar hoto
Getty Image

Jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta yi watsi da hukuncin da kotun kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke, inda ta ce za ta kalubalanci sakamakon a kotun koli.

PDP ta ce hukuncin wani karan tsaye ne ga tsarin shari’a, wanda ta ce abin kunya ne da cin zarafin bangaren shari’a a Najeriya.

Da yammacin Larabar nan ne kotun da ke zama a Abuja ta yanke hukunci cewa Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Maris, wanda suka yi takara da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Sanarwar da PDP ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Kola Ologbondiyan, ta ce ta kadu kwarai da yadda kotun ta kasa gamsuwa da hujjojin da ta gabatar kan zargin cewa Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba, kuma ba shi ya samu mafi yawan kuri’u ba.

PDP ta kara da cewa ta kadu matuka da yadda kotun ta yi watsi da dimbin shaidun da PDP ta gabatar da suke nuna cewa ba Buhari ne ya lashe zaben ba.

A cewar sanarwar ta PDP dai akwai kurakurai da dama a hukuncin.

To sai dai PDP din ta yi kira ga magoya bayanta da su kwantar da hankula, kuma kar su fitar da tsammani, domin kuwa za ta kalubalanci hukuncin a kotun koli.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...