Bola Tinubu ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin Najeriya

0

Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da ƴan jarida a fadar Also Rock bayan ya yi tattaunawa ta musamman da Shugaba Buhari a ranar Litinin.

Da ma dai ana ta raɗe-raɗin cewa jigon na APC yana son zama shugaban Najeriya, amma bai bayyana hakan da kansa ba sai yanzu, wanda a cewar kakakinsa, ya bayyana wa Shugaba Buhari ne—ƴan Najeriya kuma sai daga baya zai sanar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here