Bikin Kirsimeti: Tinubu ya rage kuɗin mota ga masu bulaguro

Shugaba Bola Tinubu a ranar Laraba ya amince da rage kashi 50 cikin 100 na farashin kudin tafiyar mota ga ‘yan Najeriya da za su yi tafiye-tafiye a lokacin bikin Kirsimeti daga ranar Alhamis, 21 ga Disamba, 2023 zuwa 4 ga Janairu, 2024.

Ministan ci gaban ma’adanai, Mr Dele Alake, ne ya sanar da hakan ga wakilan gidajen jaridu a fadar Aso Rock Villa a ranar Laraba.

Alake ya ce, “Shugaban kasa yana sanar da mu cewa daga gobe, 21 ga watan Disamba, ‘yan Najeriya da ke son yin balaguro za su iya shiga motar gwamnati ta kananan motocin bas, motocin alfarma bisa rangwamen kashi 50 cikin 100 na farashin yanzu.”

More from this stream

Recomended