BH: Kun san abin da Abubakar Shekau ya ce a sabon bidiyo?

Shekau yana yana kashe ido domin karatu
Image caption

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yana jawabi

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya sake bayyana a wani sabon faifan bidiyo, inda ya zayyana akidar kungiyar tasa sannan kuma ya yi watsi da tsarin mulkin dimokradiyya.

Faifan bidiyon na minti 35 da dakika 37 ya nuna Shekau a matsayin shugaban kungiyar Jama’at Ahl al-Sunna lil-Da’wah wal-Jihad.

A cikin bidiyon, Abubakar Shekau na zaune sanye da fararen kaya sannan yana rataye da bindiga samfirin AK47, inda yake karanto jawabin nasa daga wani kundi.

An gano tutar kungiyar ta Boko Haram a cikin bidiyon. Sannan wasu mutum biyu da suka rufe fuskarsu dauke da bindigogi na ba shi kariya.

  • Daya daga cikin ‘yan matan Chibok ta kammala digiri a Amurka
  • ‘Saura kiris sojojin Nigeria su kama Shekau suka janye’

Sai dai da alama ya samu matsalar gani kasancewar yadda yake faman kokarin karanto bayanin nasa daga kundin da ke rike a hannunsa.

Duk da cewa ba bu cikakken bayani kan hakikanin lokacin da aka nadi bidiyon, amma kwanan watan da ke jikinsa na nuna ranar 6 ga watan Mayun 2019.

wanda ya bayyana a cikiyi jawabinsa a harshen larabci ya ce burinsa ya samu magoya baya daga wajen Najeriya.

Sakon Shekau

Jagoran na Boko Haram ya ce kungiyarsa na bin sunna ne “ingantacciyar akidar musulunci,” wadda ya kamata kowane musulmi ya bi.

Shekau na ta kokarin kare akidarsa inda yake kare irin kallon da ake yi wa mabiyansa na tsattsauran ra’ayi da haifar da rikici.

Ya ce dole ne a bi Kur’ani da Sunna ba tare da sauya musu ma’ana ba.

Sai dai Shekau din ya ce tsarin mulkin dimokradiyya ya yi karo da akidar tauhidi kasancewar tsarin na nuni da fifikon tunanin dan adam bisa na Ubangiji.

Ya kuma kara da bayyana duk mutumin da yake goyon bayan Yahudawa da mabiya addinin kirista da wadanda ba musulmai ba. Hakan kuwa a tunaninsa ya halatta jininsu.

Daga karshe Shekau ya nanata irin adawar da yake yi da tsarin karatun Boko na Turawan yamma d ake koyarwa a makarantun Najeriya, inda ya ce hakan ba musulunci ba ne.

Abun fahimta a bidiyon

Image caption

Tambarin wadanda suka yi wa Shekau sabon bidiyo mai kunshe da tambarin IS

Ana ganin yin amfani da harshen Larabci da Shekau ya yi ba zai rasa nasaba da neman rike kujerarsa ta jagora ba kasancewar akwai masu tunanin idan ka iya Larabci to ka cancanci zama jagora.

Alamu sun nuna wata sabuwar kungiyar masana sadarwar zamani mai suna “Wadih al-Bayan” ce mai alaka da Boko Haram ce ta hada shi wannan bidiyo.

Sai dai tambarin da kungiyar yana da alaka da kungiyar jihadi ta IS wadda Shekau ya raba gari da ita a 2016.

Amma dai duk da hakan, Abubakar Shekau bai ambaci kungiyar ta IS ba har ya kare jawabin nasa.

Ina aka kwana kan neman Shekau?

Rundunar sojin Najeriya ta sha fadin cewa ta kashe Shekau ko kuma ta kama shi, inda yake fitowa a bidiyo ya karyata ikrarin sojojin.

A wasu lokutan ma rundunar sojin ta sha nuna wa manema labarai makaman da ta ce ta kwace daga mayakan Boko Haram har ma da tutocinsu.

A shekarar 2018 ne rundunar sojin Nigeriar ta ce za ta bayar da takuicin dala $8,000 ga duk wanda ya ba ta bayanai da za su kai ga kamo jagoran kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau.

Shugaba Buhari ya sha fadin cewa gwamnatinsa ta yi nasarar karya lagon Boko Haram.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...