BBC: An rantsar da shugaban Brazil Lula ga wa’adin mulki na uku

Lula da Silva

Asalin hoton, Getty Images

Sabon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, mai ra’ayin kawo sauyi, ya sanar da dubban magoya bayansa da suka hallarci bikin rantsar da shi a Brasilia babban birnin kasar, cewa babban aikin da ke gabansa shi ne na hada kan ‘yan kasar.

Shugaban ya ce wagegen gibin da ke tsakanin attajiran kasar da matalauta ya zama karfen-kafa ga tsarin dimokradiyya, sannan ya lashi takobin yin mulki domin kowa ne dan kasar ya amfana.
Bayan da aka kammala bikin rantsar da shi, Shugaba Lula ya shaida wa majalisar kasar Brazil cewa zai sake gina kasar daga matakin da ya kira na matsanancin lalacewa, musamman ma dajin nan na Amazon – duka karkashin matsalolin da ya gada daga Jair Bolsonaro.
Shugaba Lula ke nan ke cewa “Alhakin kulawa da dajin amazon da ma wuraren da dumbin albarkatun karkashin kasa suke kamar karfe da man fetur da tarin ruwan ruwan dadi da ke bulbulowa daga karkashin kasa da kuma hanyoyin samar da hasken lantarki wadanda ba sa gurbata muhalli.”

Ya kuma ce, “Tun da muna da ‘yan cin kai da sanin ya kamata, za mu bar dukkan mutanen duniya su amfana da wadannan albarkatun.”

(Backanno) Ya ce salon mulkin tsohon shugaba Bolsonaro ya keta sauran zaman lafiyar da ‘yan kasar ke amfana da shi – kuma ya ce kin amincewa ya sha kaye a babban zaben kasar zai raba ‘yan kasar ne kawa.

Shugaba Lula ya lashe zabe na wa’adin mulkinsa na uku ne bayan da wata kotu ta yi watsi da wani hukunci da aka yanke masa kan cin hanci da rashawa.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...