Bayan Man City ta sake lashe Gasar Firimiya: ‘Ita ce ta fi ba ni wuya,’ in ji Guardiola

Manchester City boss Pep Guardiola holds the Premier League trophy

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce nasarar ci gaba da rike kambun Gasar Firimiya a bana ita ce “mafi tsauri” a shekarun aikinsa.

City ta wartsake daga bisani inda ta lallasa abokiyar karawarta Brighton da ci 4- 1 a Filin Amex ranar Asabar, inda ta tunkude Liverpool wadda ita ma ke harin kofin da maki daya kacal.

Karo na takwas ke nan da kungiyar ta lashe wannan gasa a shekara goman Guardiola da ya yi a matsayin koci.

“Sai da muka yi nasara a karawa 14 jere kafin mu iya lashe wannan gasa,” a cewar Guardiola.

“A duk tsawon shekarun sana’ata wannan ce gasa mafi tsauri a gare ni, da gaske.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pep Guardiola has won three La Liga titles, three Bundesligas and two Premier League titles

A watan Janairu ne Liverpool ta je filin wasa na Etihad tana jan ragamar tebur da maki bakwai amma sai Man City ta cinye ta 2-1.

Bayan rashin nasarar da ta yi da ci 2-1 a hannun Newcastle gaba a wannan wata, Man City ta lashe gasar bana bayan ta samu nasara a wasa 14 da ta buga jere.

Liverpool dai ta kare kakar wasannin bana da maki 97, na uku mafi yawa da aka taba samu a tarihin kwallon kafar Ingila – kasan Man City wadda ta lashe gasar da maki (98) da kuma a bara inda ta hada maki (100).

“Tabbas sai na taya Liverpool murna, ina gode musu kwarai da gaske,” Guardiola ya fada wa Sky Sports.

“A bara Manchester City ta kai ga wani matsayi. Sun taimaka wajen kara mana kaimi inda muka kara matsa wa gaba daga inda muke a bara.

“Karawa da wannan kungiya ta kara mana kaimi don wajen abin da muka yi. Abin al’ajabi ne, hada maki 198 a kakar wasa biyu.

“Yawanci idan ka samu maki 100 mai yiwuwa ne ka koma baya amma sai Liverpool ta taimake mu muka rike wuta.”

Guardiola ya lashe gasar La Liga uku jere a shekara ukunsa na farko da ya yi a Barcelona da kuma lashe kofin Bundesliga uku jere a shekara ukun da ya yi a Bayern Munich kafin ya koma City.

Manchester United ce kungiyar da kadai ta taba lashe Gasar Firimiya sau uku a jere ta kuma sake yin haka sau biyu, daga kakar 1998-99 zuwa 2000-01 da kuma 2006-07 zuwa 2008-09.

More News

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama ƴan fafutukar kafa ƙasar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...

Wata mata ta mutu bayan da kwantena ta faɗo kan motar da take ciki

Wata kwantena mai tsawon ƙafa 40 dake maƙare da kaya ta faɗo kan wata ƙaramar mota ƙirar Nissan mai rijistar namba ABJ 692 BG...